3 Afirilu 2022 - 20:20
Shugaban Kasar Iran Ya Aikewa Da Shugabannin Kasashen Musulmi Sakon Murnar Shigowar Wata Azumin Ramadana Mai Alfarma

Shugaban Kasar Iran Ya Aikewa Da Shugabannin Kasashen Musulmi Sakon Murnar Shigowar Wata Azumin Ramadana Mai Alfarma.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sakon ya kunshi yin ishara da muhimmancin watan na Azumin Ramadhan wanda yake kunshe da daren-lailatul-qadari, wanda kuma wata ne da aka sauko da alkur’ani a cikinsa.”

Har ila yau shugaban kasar ta Iran, Ibrahim Raisy ya ce; wannan watan wata dama ce gagaruma ga dukkanin musulmi da su tsarkake kawukansu, su kuma bunkasa ruhinsu da imaninsu.”

Wasikar ta shugaban kasar Iran zuwa takwarorinsa na kasashen musulmi ta kuma kunshi nuna fatan ganin an sami cikakken hadin kai a tsakanin musulmin domin karfafa aiki tare da kuma hadin kai.

Bugu da kari, shugaba Ibrahim Ra’isy ya yi fatan ganin hadin kai a tsakanin kasashen musulmin ya kawo karshen ta’addanci da akidar kafirta musulmi da kuma tabbatar da zaman lafiya a duniya baki daya,musamman a Palasdinu.

342/